<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>55</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Uba na cikin Sama,
 Sunanka mai tsarki ne,
 Mulkinka shi zo, ya AlIah,
 Yadda ka ke marmari.

[V2]
 2) Duk abin da ka ke nufi
 Sai mu aikata a nan,
 Kamar yadda a ke yinsa
 Cikin gidanka a can.

[V3]
 3) Ba mu yau abincin yini,
 Bisa ga alherinka.
 Alhini ba za mu yi ba,
 Sai mu yi bangaskiya.

[V4]
 4) Gafarta kurakuranmu,
 Na junanmu za mu yi.
 Daga jaraba da mugu,
 Tsare mu, Mai Cetonmu.

[V5]
 5) Girma, iko, duk da mulki
 Naka ne har abada.
 Cikin sunan Almasihu
 Muna roƙonka. Amin.</lyrics>
<title>Ya Uba Na Cikin Sama LW55</title>
</song>